Bacci Da Rana A Ramaḍān
Dayawan mutane suna zama ido biyu cikin daren Ramadana. Wasun su suna tafiyar da gaba daya daren a abubuwa marasa amfani. Wasu suna tafiyar da duka darensu a aikata zunubi.
Siffofi da Fa’idoji Bakwai Da Ramadana Ya Kebanta Da Su.
Fa’idar da za a dauka daga wannan shi ne cewar karanta Qur’āni a wannan watan ya fi falala akan sauran watanni. Duk da cewar abun so ne ga musulmi ya yawaita karanta Qur’āni a dukkan sauran watanni, amma wannan watan, watan da acikinshi aka saukar da Qur’āni, watan da jibreel (alaihis salam) (ya kasance) yakan zo su yi Muraja’ah Qur’āni da annabi (ﷺ), wannan watan yana da falala mai girma game da karatun Qur’āni.