Duʾâ: Ya Allâh! Na Zalunci Kaina Zalunci Mai Yawa
Abû Bakr (رضي الله عنه) ya ce: "Na ce wa Manzon Allâh (ﷺ): "Ya Manzon Allâh! Koya min addu'a da zan rinƙa fada a sallah ta" sai ya ce: "ka ce:
اللَّهُمَّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي ظُلْمًا كَثِيرًا وَلَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ فَاغْفِرْلِي مَغْفِرَةً مِنْ عِنْدِكَ وَارْحَمْنِي إِنَّكَ أَنْتَ الغَفُورُ الرَّحِيمُ
Allāhuma inni zhalamtu nafsi zhulman katheeran wa laa yaghfiruz zhunuba illaa anta faghfir lii maghfiratan min indika warhamnii innaka antal ghafurur Raheem.
Ya Allâh! Na zalunci kaina zalunci mai yawa, kuma babu wanda ya ke yafe zunubi faace Kai, domin haka Ka yafe min, ka yi min Rahama (ka jiƙai na), Lallai, kai mai Gaafara ne (Mai yafiya) , Mai Rahama.”
Daga: Bukhâri 6953, Muslim 2705
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar Turancin Salafi Centre of Manchester