Kaiwa Zuwa Ramadana Ni’ma Ce
﷽
Babban Malamin Nan Al-Ḥāfiẓ Ibn Rajab (رحمه الله) ya ambata,
“Kaiwa zuwa watan Ramadana da azumtar shi babbar ni’ima ce ga wanda Allāh ya bashi ikon yin hakan.
Abunda yayi nuni ga hakan shi ne Hadisin mutane uku, wadanda biyu daga ciki sukayi mutuwar Shahada na ukun kuma ya mutu akan gadonshi bayan (mutuwarsu), kuma aka ganshi a mafarki cewa ya wuce su, sai Annabi (ﷺ) ya ce:
“Shin ba ya sallaci salloli adadi kaza da kaza bayansu ba, Kuma ya kai watan Ramadana ya azumce shi? Na rantse da Wanda raina ya ke hannun Shi, tsakanin shi da su (nisa ne) da ya fi nisan da ke tsakanin sama da kasa.”
Imām Aḥmad Da Wasunsa Suka Rawaito.
Mukhtasar Latāif Al-Ma'ārif sh. 118
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin Markaz Mu’ādh ibn Jabal (UK)