Mutum Yana Tsakachi Da Yin Sahur Sai Mai Kiran Sallah (Al-Mu’adhin) ya Kirawo Sallah


Tambayar da akayiwa Shaykh Al-ʿAllâmah Muqbil ibn Hâdi Al-Wâdi'î (رحمه الله): 

Idan mutum tana tsakachi da yin sahur Sai mai kiran sallah ya kirawo sallah (ta asuba) - shin ya wajaba akan mutum ya tofar da abunda ke bakinshi ko kuma ya ci ya hadiye shi?

Amsa: 

"Dangane da abunda yake bakinshi, ba zai tofar da shi ba, amma ba zai ci wani abu bayan shi ba, sedai idan yana rike da ruwa (ko wani abun sha da yake hannunshi). Wannan saboda abunda aka rawaito a Sunan Abû Dâwûd daga Abû Hurayrah (رضي الله عنه) cewa Manzon Allâh ‎(ﷺ) ya ce: "idan Mai Kiran Sallah ya kira sallah kuma a hannun dayanku akwai mazubi (na ruwa) ya sha daga cikinshi abunda ya ke bukata." Domin haka babu laifi idan ya sha yayin da Mai Kiran Sallah ya kira sallar (asuba) da sharadin cewa ruwan ya riga da yana hannunshi."


Daga: Fadâ'ih wa Nasâ'ih, shafi 76.
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga fassarar turancin ʿAbdulWâhid Alam.
Previous
Previous

Duʾâ: Ya Allâh! Na Zalunci Kaina Zalunci Mai Yawa

Next
Next

Siffofi da Fa’idoji Bakwai Da Ramadana Ya Kebanta Da Su.