Siffofi da Fa’idoji Bakwai Da Ramadana Ya Kebanta Da Su.


Al-ʿAllâmah Sâlih bn Fawzân Al-Fazwân (‏حفظه الله) ya ce:

Haƙiƙa fa'idojin watan Ramadana suna da yawa, daga cikin su:

1) Ana Tsayar Da Daya Daga Cikin Rukunan Musulunci A Watan Ramadana

Allâh ya ware Ramadana domin aiwatar da rukunin (azumi) daga rukunan musulunci. Wannan ya isa ya nuna mana darajar wannan watan.

2) An Saukar Da Qur’âni A Watan Ramadana

﴾شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِيَ أُنزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ﴿

Watan Ramadana wanda aka saukar da Qurʾâni a cikinsa. (Al-Baqarah: 185)

Wannan falala ce mai Girma, wane lokacin aka keɓe da saukar da Littafin Mafi girma, (Qurʾâni) daga Litattafan Allāh.

Fa'idar da za a dauka daga wannan shi ne cewar karanta Qurʾâni a wannan watan ya fi falala akan sauran watanni. Duk da cewar abun so ne ga Musulmi ya yawaita karanta Qurʾâni a dukkan sauran watanni, amma wannan watan, watan da acikinshi aka saukar da Qurʾâni, watan da Jibreel (عليه سلام) (ya kasance) yakan zo su yi Muraja'ah Qurʾâni da Annabi (‎ﷺ), wannan watan yana da falala mai girma game da karatun Qurʾâni. Tsawon dukanin shekara ladan (karanta) harafi ɗaya shi ne lada goma, amma yayin Ramadana ana ninka wannan. 

3) Daren Laylatul Qadari Yana Cikin Ramadana

Wannan watan ya kunsa a cikin shi, wani dare da ya fi wata dubu falala. Saboda haka duk wanda yayi sallah ya bautawa Allâh a wannan dare, yana mai neman ladanShi, za a saka mishi da dai-dai (sakamakon ladan) wata dubu. Idan mukayi lissafin wannan a shekaru zamu iske cewar ya fi shekara tamanin, tsawon wannan lokacin (zai zama) kamar mutum yana cikin bauta da ɗa'a ga Allâh.

4) Ana Ruɓanya Lada A Ramadana

Daga falala da siffofin dasuka kebanta ga wannan watan shi ne kasancewar ayyuka na kwarai ana nunka su a lada da yawa, sama da sauran watanni wannan saboda darajar watan ne. 

5) An Kebanta Ramadana Da Yin Sallar Tarawi (Tarawîh) Cikinsa: 

Allâh ya ware wannan watan da tsayar da sallar tarawi, wadda ake yin jam'in ta a masallatai, kuma wannan ba ya da ruwa a sauran watanni. Wannan yana nuna mana falalar da matsayin wannan watan a wurin Allâh.

6) Ana Bude Ƙofofin Aljanna Kuma Ana Rufe Ƙofofin Wuta

Yayin watan Ramadana ana bude ƙofofin aljanna domin karban kyawawan ayyuka da masu aikata su, su kuma ƙofofin wuta ana kulle su sannan ayyukan saɓo da zunubai na raguwa a wannan watan.

7) Ana Ɗaure Sheɗanu A Sanya Musu Mari

Allâh yana kange muminai daga sheɗanu a wannan watan, saboda haka ba sa lalata musu bauta, sanadiyar wannan ne zaka tsinci mutune suna dagewa wajen ayyukan ibaadu, hatta waɗanda ɗabi'arsu a sauran (watannin) shekara shi ne ƙyuya da sakaci. Sai ka gansu sun himmatu wajen ayyukan ibaada a watan Ramadana, wannan abu ne a fili (kuma sananne).

Hakan ya kasance ne saboda an ɗaure shedanu daga ma'abota imani. Amma dangane da kafirai da munafukai kuma, haƙiƙa shedanu suna da karfin iko a kansu a cikin Ramadana da wajen shi.

Muna rokon Allâh (Mafi ɗaukaka) ya albarkace mu, da kyakyawan albarkatun Ramadana, ya sanya mu daga cikin waɗanda suke fa'idantuwa daga falalolinsa da sakamakonsa, kuma muna rokon (Allâh) kar da ya haramta mana falalarsa da ladansa, kuma kar ya haramta mana (damar) aikata ayyukan alheri a cikin wannan watan da waninsa. 


An dauko kuma an takaita daga: Majâlis Shahr Ramadan Al-Mubârak na Shaykh Al-Fawzân sh.8-11 
Fassarar AMMAN CIRCLE Editorial daga Salafi Center Manchester
Previous
Previous

Mutum Yana Tsakachi Da Yin Sahur Sai Mai Kiran Sallah (Al-Mu’adhin) ya Kirawo Sallah