Tafsir: Kai Kaɗai Muke Bautawa Kuma Daga WurinKa Kaɗai Muke Neman Taimako. Ash-Shaykh Ibn ʿUthaymîn
Ma'ana, "ba ma neman taimakon kowa a ibaada ko wani abu koma bayan haka." Wannan "neman taimakon" shi ne neman tallafi, da taimako, kuma Allâh (سبحانه وتعالى) ya haɗa tsakanin bauta (ibaada) da kuma neman tallafi ko tawakkali (dogaro akan Allâh) a wurare masu dama cikin Qur'ãni.
Asulan Tauhidi - 2 - Ina Zamu Fara?
Kuma ba mu aika gabaaninka (ya Muhammad) annabi ba faace sai da muka yi mishi wahayi cewa “babu abun bautawa da gaskiya sai Ni (Allâh) domin haka ku bauta min” (Sûrah Anbiya: 25)
Asulan Tawhidi - 1 - Tawhidi Shi Ne Tushen Addini
Qur'âni yayi umarni da bautar Allâh shi kaɗai, ba tare da kishiyoyi ba, kuma yana hani ga shirka. Wannan shi ake kira tawhidin ayyuka da ad-du'a (Al-Tawhîd Al-'Amalî At-Talabi) wato mutum ya sanya ayyukan bautarshi su zamanto na Allâh shi kaɗai, kuma ba ya neman kowa da addu'arsa, neman taimakonsa, neman mafaka, neman agaji da sauransu.
Matsayin Tawhidi Ga Zukãta
Zukata suna bukatar Tauhidi! Kuma shine, a keɓe dukkan bauta ga Allãh (سبحانه) Shi kadai.